Music: Ademola Tarka/Hamisu Said Yusuf/Ali Jubril Namanjo Baby ina kwana Baby ina gajiya Shin kin tashi lafiya Rabin raina Soyayya da ƙafiya Nake miki kin jiya Tabbas kin iya soyayya Rabin raina Da ma da ke na fara haɗuwa da na yi aure tuntuni Zama dake akwai ƙaruwa haƙiƙa ni kina burge ni Da ma da ke na fara haɗuwa da na yi aure tuntuni Zama dake akwai ƙaruwa haƙiƙa ni kina burge ni wayyo Soyayya na da daɗi Lobayya na da daɗi Amma dake tafi daɗi wayyo Soyayya na da daɗi Lobayya na da daɗi Amma dake tafi daɗi wayyo Da ma za ki yarda da duk batunsa na soyayya ne Ke ma ki amince da ƙudurinsa na alheri ne Wanda tasiri ne A zuciya ki zaune Ya ba ki zuciya ta yi duka kyauta autar ma Zan so ki bi yarda Ki gaya masa kin ragi tsada Ni batun na jaddada ki gwada min za ki mutulta Ki dakata ki ji ’yan mata A yau bikinku muke fata Mun shaida kun zama ’yan gata Ki tausawa masa raina Кaunarki ta kama ni tun farko Ni fatana ni da ke mu yi ƙarƙo Aurenmu da ni da ke ya yi ƙarƙo Mu haifi yaya masu albarka Da ma da ke na fara haɗuwa da na yi aure tuntuni Zama dake akwai ƙaruwa haƙiƙa ni kina burge ni Da ma da ke na fara haɗuwa da na yi aure tuntuni Zama dake akwai ƙaruwa haƙiƙa ni kina burge ni wayyo Soyayya na da daɗi Lobayya na da daɗi Amma dake tafi daɗi wayyo Soyayya na da daɗi Lobayya na da daɗi Amma dake tafi daɗi wayyo Soyayya daɗi Soyayya daɗi Soyayya daɗi Soyayya daɗi